Najeriya: Gwamnati ta hana hakar ma′adanai a jihar Zamfara | Labarai | DW | 07.04.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: Gwamnati ta hana hakar ma'adanai a jihar Zamfara

A wannan Lahadin gwamnati ta bayar da umarnin dakatar da duk wani aiki na hakar ma'adanai a jihar Zamfara da ke fama da ayyukan 'yan bindiga da suka yi sanadiyar rayuka tare da jefa jama'a cikin yanayi na fargaba.

Wani mai bai wa shugaban kasar shawara, Bashir Ahmed ne ya wallafa sanarwar a shafinsa na twitter a wannan Lahadin, umarnin da ke zuwa a daidai lokacin da jihar ke cikin yanayi na tashin hankali a sanadiyar hare-haren 'yan bindaga da ya lakume rayuka da yadda ake ci gaba da satar mutane.

Wata majiya kuwa, ta ce an dauki matakin ne bayan da aka danganta maharan da ke kai wadannan hare-haren da wasu masu aikin hakar ma'adanan ta hanyar ba ta dace ba. Jihar Zamfara fiye da sauran jihohin Najeriya, ta fuskanci tashin hankali mafi muni tun bayan da aka shiga wannan shekarar ta 2019, inda ta tafka asarar rayuka da dukiya tare da kasancewar jama'a cikin yanayi na fargaba a sanadiyar ayyukan 'yan bindiga.