Najeriya: Gurbacewar muhalli a yankin Niger Delta | Siyasa | DW | 15.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya: Gurbacewar muhalli a yankin Niger Delta

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta kasa da kasa Amnesty Internation ta bayyana sakamakon wani bincike kan yadda wasu kamfanonin aikin mai a yankin Niger Delta wato Shell da Eni ke haddasa gurbacewar muhali.

Kungiyar ta Amnesty International ta ce ta dau lokaci tana tuntuba da kuma sa wasu kafofin kimiyya bincike na kwakwaf kan yanayin tsiyayar man fetir a yankin Niger Delta wanda ya gurbata muhalli. Kungiyar ta ce sakamako ya nuna cewar manyan kamfanoni biyu musamman su Shell da Eni na aikata mummunar barna ta fannin haddasa tsiyayar mai yayin ayyukansu na fidda danyan mai a yankin. Bayan haddasa tsiyayar ta mai, kuma kamfanonin kan yi jan kafa wajen kokarin ziyartar inda aka gano mai din na tsiyaya don su yi abin da ya kamata kan lokaci.

Kamfanonin na Shell da Eni sun yi ta nanata cewar suna iya bakin kokari wajen kare afkuwar tsiyayar man daga ayyukan da suke yi na hako danyan mai, tare da alakanta tsiyayar ta mai da halayyar 'yan satar danyen man. Kungiyar ta Amnesty ta ce kungiyoyin na Shell da Eni ba sa nuna kulawa sosai kan tsiyayar mai da suke haddasa kuma hakan ya na nakasu ga al'ummomin yankin wadanda gonakinsu suka shafu abin da ya janyo cikas ga harkokin noma da kamun kifi.

Sauti da bidiyo akan labarin