Najeriya: Gudunmawar ′yan kato da gora wajen samar da tsaro ga al′umma | Zamantakewa | DW | 30.04.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Najeriya: Gudunmawar 'yan kato da gora wajen samar da tsaro ga al'umma

'Yan kato da gora da aka fi sani da Civilian JTF a Najeriya suna taka muhimmiyar rawa wajen kare al'umma daga ta'asar 'yan bata gari.

Sakamakon yadda ake garkuwa da mutane a wasu wurare kan hanyar Zamfara zuwa Sakkwato, 'yan kato da gora wato Civilian JTF da gwamnatin jihar Zamfara ta dauka na ba da tsaro iya gwargwado, a madadin jami'an tsaro da ke da alhakin yin hakan. Sai dai 'yan JTF din na fuskantar kalubalen rashin makaman da za su iya tinkarar 'yan bindigar.

Titin kwanar dogon karfe daya daga cikin manyan hanyoyin da motoci ke yawan bi kuma daya a cikin inda 'yan kato da gorar ke tsayawa, wuri ne dai da 'yan bindigar ke tare mutane domin yin garkuwa da su. Muhammad Sani Jabaka na daga cikin 'yan kato da gorar da ya nuna amfanin tsayawarsu a wurin da cewa koda wani mugu ya tinkaro ya hange su zai san hanyar da zai bi.

Wasu daga cikin 'yan kato da gorar sun ce wannan aiki suna yinsa iya bakin ransu, burinsu shi ne al'umma sun zauna lafiya. Saboda jajircewarsu yasa aka samu gagarumar nasarar fatattakar 'yan bindigar da ke tare mutane a kan hanyoyin inji Lauwali Usman.

"Mun samu nasara sosai. Munsha cin karo da 'yan bindiga mu kama na kamawa a kashe na kashewa. Mu ba mu gudu ba mu ja da baya saboda mun ji za mu iya ne, ba kiranmu aka yi ba, mu muka ga dama muka sa kanmu sannan duk ke nan wurin ko an tinkare shi da ita ba ta tashi."

Nan dai wasu 'yan Civilian JTF ne a yaki da Boko Haram a Arewa maso Gabacin Najeriya

Nan dai wasu 'yan Civilian JTF ne a yaki da Boko Haram a Arewa maso Gabacin Najeriya

Wannan aiki a kan hanya da 'yan kato da gorar ke yi ana ganin aiki ne na jami'an tsar. To ko me jami'an tsaron jihar ta Zamfara za su ce kan hakan? SP Shehu Muhammed shi ne kakakin rundunar 'yan sandan jihar Zamfara.

"Maganar cewa 'yan kato da gora ko kuma Civilian JTF suke ba da tsaro kan hanyoyi ko kuma dakile 'yan bindiga ban da masaniyar wannan, amma abin da ke akwai shi ne muna aiki tare da su, suna taimaka wa jami'an tsaro da muhimman bayanai na wadannan miyagu saboda sun san inda wadannan mutane suke fiye da jami'an tsaro."

To ko yaya masana harkar tsaro ke kallon yadda 'yan kato da gorar ke tsayawa bakin titi don ba da tsaro? Manjo Muhammed Bishir Galma mai murabus masanin tsaro ne a Najeriya da ya ce.

"Abin nan yana nuna kamar akwai rudu cikin lamuran irin wadannan mutanen da aka sani suke kara ruda abin da ke faruwa saboda haka suma yan ta'addar suna iya zuwa su bude wani wuri suce suma 'yan banga ne."

Sakamakon kalubalen tsaro da jihar Zamfara ke fuskanta ya sa gwamnati jihar a baya ta dauki 'yan kato da gorar 500 a kowace masarauta cikin masarautu 17 na jihar, wanda yawan ya kai 8500 kuma tana biyansu Naira dubu 15 a kowane wata duk don kwanciyar hankalin al'ummar jihar.