1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gobarar ta janyo asarar rayuka da dukiya

Abdullahi Maidawa Kurgwi
September 10, 2018

Mutane da dama sun mutu a sanadiyar wata gobara da ta tashi a wani gidan mai a safiyar wannan Litinin a garin Lafiya da ke a jihar Nassarawa.

https://p.dw.com/p/34caM
Nigeria Terror Anschlag Abuja
Hoto: Reuters

Wasu shedun gani da ido, sun ce gobarar ta tashi ne a kusa da wata masana'antar sarrafa iskar gas, inda nan take ta zarce zuwa wani gidan mai da ake kira Watson filling station.

Ya zuwa yanzu dai babu alkaluma na adadin mutane da suka mutu ko suka sami rauni daga hukumomin jahar, amma wa ta majiya ta ce an garzaya da mutane fiye da arba'in zuwa asibiti a sanadiyar raunin da suka samu daga gobarar.