Najeriya: Dokar hana fitar dare a jihar Abia | Labarai | DW | 13.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: Dokar hana fitar dare a jihar Abia

Gwamnatin jihar Abia Okezie Ikpeazu da ke Kudu maso Gabashin Najeriya ta dauki dokar hana fitar dare sakamakon rikicin da ya barke tsakanin sojoji da 'yan Biafra.

Nigeria Onitsha Vertreter der Organisation zur Abspaltung von Biafra MASSOB (Getty Images/AFP/P.U. Ekpei)

Masu rajin kafa kasar Biafra a birnin Onitsha na Najeriya

Cikin daren Talata wayewar Laraba ne dai Gwamnan jihar Abia Okezie Ikpeazu ya sanar da matakin hana fitar daran daga karfe shida na yamma zuwa Shida na safe har ya zuwa ranar Juma'a. 'Yan kwanakin baya-bayan nan dai an samu arangama sosai tsakanin masu rajin kafa kasar ta Biafra da sojoji, da sauran jami'an tsaron na Najeriya. A ranar Lahadi da ta gabata kungiyar ta IPOB ta ce an kashe mutanenta guda biyar, batun da rundunar sojojin ta Najeriya ta karyata. Sannan kuma IPOB din ta ce da safiyar yau Laraba sojoji sun yi wa gidan na Nnamdi Kanu a birnin Umuahia da ke cikin jihar Abia kawanya, sannan an kashe wasu daga cikin magoya bayan 'yan IPOB din hudu da suka yi yunkurin tare wa sojojin hanya.