1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukunci kan neman magani da kudin gwamnati

February 10, 2022

'Yan majalisar dokokin Najeriya na shirin kafa wata dokar da ta tanadi tarar miliyoyin Naira ko kuma daurin shekaru bakwai, ga masu laifin kwashe kudin gwamnati da sunan neman lafiya a kasashen waje.

https://p.dw.com/p/46qDA
Najeriya I Shuga Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHoto: Julien de Rosa/ Pool/REUTERS

Kusan dalar Amirka miliyan 500 ne manyan jami'ai da sauran 'yan boko ke batarwa a shekara a Tarayyar Najeriyar da nufin zuwa kasashen Turai, domin neman magani na cutuka iri-iri. Kuma mafi yawan masu ziyarar na zaman manyan jami'an gwamnati a matakai dabam-dabam, abun kuma da majalisar tarayyar kasar ke neman sauyawa tare da  kokarin kafa wata dokar da ta tanadi daurin shekaru bakwai ko kuma tarar Naira miliyan 500 kan kowane jami'in gwamnatin da ya kwashi kudin gwamnati domin neman lafiyar. Sabuwar dokar da ta haura karatu na biyu a zauren majalisar wakilan kasar dai, na da burin ingantar  tsarin lafiya a Najeriyar da asibitoci ke korafin rashin kayan aiki da magani. Dokar dai ta ce ba wani jami'in gwamnati da zai kai fita wajen kasar domin duba lafiya ko kuma asibiti, har sai ya samu amincewar wata hukuma ta musamman a karkashin jagorancin ministan lafiya a matakin tarayya ko kuma kwamishinan lafiya a jihohi. Ko bayan kisan kudi na hukuma dai, akwai fatan yin dokar na iya sauya yanayin asibitocin kasar da ke lalace.

Najeriya I Gombe
Asibitocin Najeriya da dama na fama da tarin matsaloliHoto: picture-alliance/dpa

Sanata Ali Ndume dai na zaman dan majalisar dattawan kasar da kuma ya ce, akwai bukatar mai da kai ga hanyar toshe sata da nufin hana fitar kudi da sunan neman lafiya. Koma ya zuwa ina 'yan boko da jami'an gwamnatin ke shirin su kai da nufin hakuri da rashin kyawun tsarin lafiya a Najeriyar, kasafin da kasar ke warewa a shekara ga batun lafiya bai taka kara ba balle ya kai ga kwantar da hankalin 'yan bokon. Kuma a fadar Dakta Umar Tanko da ke zaman kwararre kan harkar lafiyar al'umma da kamar wuya iya kai wa ya zuwa nasarar dokar a kasar da 'yan siyasar ke danyen ganye da masu takama da rikon biron na gwamnati. Doka domin gyara ko kuma dodo-rido dai, wannan ne karo na farko da masu dokar ke dora hukunci kan neman gyara a tsarin lafiyar al'ummar kasar. Kama daga manyan asibitoci na matakin tarayya ya zuwa 'yan uwansu da ke a unguwannin kasar dai, kusan daukacin asibitocin Najeriyar na bukatar sauyin fasali da nufin dacewa da zamani baya ga matsala ta karancin albashi da ta tilasta daruruwan kwarrarun likitoci ficewa daga kasar zuwa cin rani. Kuma a ta bakin Dakta Ado Mohammad tsohon shugaban Hukumar Lafiya a Matakin Farko na kasar, sabuwar dokar na iya sauya da dama a cikin kasar a halin yanzu.