1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: An koma yin rijista wayar salula

April 16, 2021

Gwamnatin tarrayar Najeriya ta dage haramcin rijistar wayar salula a kasar. Mahukunta na Abuja sun ambato batun rashin tsaro a kan gaba a cikin matakin tsaida rijistar katin na salula.

https://p.dw.com/p/3s8Lf
Afrika | Mobile money
Hoto: picture-alliance/dpa/Godong

A cikin watan Disamban da ya shude ne dai gwamnatin kasar ta tsaida shirin tare da tilasta 'yan kasar yin rijistar daukaci na layukansu da lamba ta dan kasa da gwamnatin ke fatan na iya kaiwa ga rage yawan aikata laifuka cikin kasar.Tarrayar Najeriyar dai na da akalla layin na salula miliyan kusan 200 da damansu ko dai ba su da rijistar ko, kuma ke da bambamci a tsakanin masu rijistar asali da masu amfani da layukan wajen sadarwa yanzu. Ana dai zargin amfani da salular wajen satar al'umma da karbe kudin fansa  dama raguwa na manya na laifuka a tarrayar Najeriya a lokaci mai nisa, kafin matakin da masu mulkin ke fatan na iya rage aikata laifuka tsakanin al'umma.To sai dai kuma wattani Hudu baya, gwamnatin kasar ta ce ta fara ganin alamun haske cikin matakin da yake  kan hanyar warware aikata laifukan da ke dada sauya salo da komawa na zamani.

Shirin ya yi tasiri wajen samun raguwar aikata miyagun laifuka na yin garkuwa da mutane

Afrika | Mobile money
Hoto: Getty Images/AFP/Y. Chiba

Damuwa cikin aikata laifi ko kuma hana 'yan kasa su wataya, shirin tsaida rijistar dai ya kai ga tada hankali na 'yan kasar da suka rika share kwana da kwanaki suna layin neman tsira da layukan na salula da ke zaman abokan harka. A karon farko dai yawan wayar layukan salular sun sauka ya zuwa miliyan 173 daga sama da miliyan 200 da yake kafin dauka na matakin. Har ila yau dai kamfanonin sun ce sun yi asarar da ta kai ta kusan Naira miliyan dubu 25 a tsawon watanni guda hudu. Ga shi kansa batun tsaron dai kuma a fadar kabiru Adamu da ke sharhi bisa tsaron,da sauran aiki a tsakanin 'yan mulkin da cika burin kai karshen amfani da salular wajen aikata laifi a cikin tarrayar Najeriyar.n Ko ya take shirin da ta kaya a tsakanin gwamnatin da ke neman gyara tsaro da kamfanonin sadarwa da ke mai da fifiko bisa riba. Da kyar da gumin goshi ne kamfanin MTN da ke zaman mafi girma a kasar ya tsira a hannun 'yan mulkin da suka ci tararsa dalar Amirka miliyan dubu hudu bayan gaza yin rijistar wasu layuka miliyan kusan biyar .