1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aniyar magance kyamar baki

Zulaiha Abubakar
March 13, 2017

Kasashen Najeriya da Afirka ta Kudu sun dauki aniyar magance kyamar baki ta hanyar kirkirar wata cibiyar fadakarwa da wayar da kai.

https://p.dw.com/p/2Z78q
Südafrika Xenophobie Rassismus Unruhen
Hoto: Getty Images/G.Guercia

Kasashen Najeriya da Afrika ta kudu sun dauki aniyar magance 'kyamatar baki ta hanyar kirkirar wata cibiyar fadakarwa da wayar da kai kamar yadda Ministar harkokin kasashen wajen Afirika ta Kudu Maite Nkoana-Mashabane ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP, a Pretoria a lokacin da take ganawa da takwaranta na Najeriya Geoffrey Onyeama kan matakan kariya ga 'yan Najeriya da ke zaune a kasar ta Afrika ta kudu.


A watan da ya gabata ne 'yan kasar ta Afrika ta Kudu suka fara afkawa Duk wani dan Afrika bakar fata dake zaune a kasar tare da kone masu guraren kasuwancin su kodayake wasu 'yan kasar sun bayyana cewar ba ko ina aka kai farmakin ba sai guraren saye da sayar da miyagun kwayoyi. Shidai wannan mummunan hari da 'yan Afrika ta kudu suka kai wa baki yayi sanadiyyar rasa rayuka da kuma kone shaguna kusan ashirin mallakar 'yan Najeriya.

Südafrika Pretoria Proteste
Hoto: picture-alliance/Photoshot/Z. Jianlan

A daya bangare Geoffrey Onyeama wanda kuma shi ne wakilin Najeriya a ganawar ya shaida wa manema labarai bayan kammala taron cewar yana da tabbacin 'yan Najeriya za su cigaba da zama a kasar ba tare da wata barazana ba inda ya kara da cewar akwai 'yan Najeriya sama da dubu dari takwas a kasar ta Afirika ta Kudu a halin yanzu.