1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Biyan diyya ga yankin Ogoni na Najeriya

Ramatu Garba Baba
February 12, 2019

Wasu mata 'yan Najeriya hudu sun shigar da karar kamfanin Shell a gaban kotun hukunta manyan laifuka ICC, bisa zargin kamfanin da hannu a kisan da aka yi wa mazajensu karkashin mulkin soja a shekarar 1995.

https://p.dw.com/p/3DFCr
Jagoran gwagwarmaya Ken Saro-Wiwa
Jagoran gwagwarmaya Ken Saro-WiwaHoto: picture-alliance/dpa

Daya daga cikin matan, Esther Kiobel da ke zaman uwar gidan Barinem Kiobel da aka rataye tare da marubuci kuma jagoran gwagwarmayar nemar wa yankin diyya kan barnar da kamfanin ya haddasa, Ken Saro-Wiwa ta nemi taimakon kotun don ganin an bi musu hakkinsu tare da biyansu diyya.

Ta zargi Shell da laifin taimakawa gwamnati wajen kamo mijinta da sauran wadanda aka hallaka su tare, bayan da suka jagoranci gangamin adawa da illolin da malalar mai ke yi, ga al'ummar da ke rayuwa a Ogoni na yankin Naija Delta, gangamin da gwamnatin marigayi Janar Sani Abacha ta ce barazana ce ga tsaron kasar. Aiwatar da hukuncin kisa kan Ken Saro-Wiwa da sauran abokan gwagwarmayarsa da gwamnatin Najeriya ta wancan lokacin ta yi, ya haifar da suka dama cece-kuce a ciki da wajen kasar.