1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Buhari ya yi taron farko da ministoci

Ubale Musa/ GATNovember 6, 2015

Ganawar da ke zaman irinta ta farko a tsakanin shugaban kasar da ministocin dai ta maida hankali ga kokarin samo hanyoyin tunkarar jerin kalubalen dake gaban Najriyar.

https://p.dw.com/p/1H0oR
Präsident von Nigeria Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu BuhariHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

A wannan Alhamis fadar gwamnatin Najeriya ta Aso Rock ta gudanar da taronta na farko da sababbin ministoci na gwamnatin kasar.

Ganawar da ke zaman irinta ta farko a tsakanin shugaban kasar da majalisar ministocin dai na maida hankali ga kokarin samo hanyoyin tunkarar jerin kalubalen dake gaban 'yan canjin da suka dauki alkawarin zuma da madi a cikin akushin kowa, amma kuma ke fuskantar zahiri ta rashin kudin dake fuskantar kasar a halin yanzu.

Kalubalen kuma da shi kansa shugaban kasar bai boye ba ga ladanan sauyin dake shirin share kwanaki har biyu suna neman hanyar fitar da wando ta tsakar ka.

Jawabin Shugaba Buhari a gaban ministocinsa

"Aikin gyaran kasa da sake farfado da al'amura na zaman na gaggawa kuma mai girma sannan fata na 'yan kasa ma na da yawan gaske. Karfin zuciyarmu na kaiwa ga cin nasarar sauya makomar kasarmu dole ne ya zamo daidai da kalubalen"

Jan aikin da ke gaban jeri na ministocin 36 dai na zaman sake dauko tattalin arzikin dake cikin laka ya zuwa yanzu tare da dorashi a bisa turbar da 'yan kasar ke iya alfahari kansa, sannan kuma da fadada hanyoyin samun kudin shiga daga man fetur banda batun tsaro da ababen more rayuwar da ke zaman babban alkawarin 'yan sauyin da kuma har yanzu ke tsakiyar zuciya ta gwamnatin a fadar Dokta Hakeem Baba Ahmed da ke zaman jagoran hada taron.

Unabhängigkeitstag in Nigeria 2015
Shugaba Buhari da Bukola SarakiHoto: DW/U. Musa

Batutuwan da taron ya tattauna kansu

"Muna son mu tada tattalin arzikin Najeriya ta yanda talauci zai ragu a kasar. Muna son mu rage karan tsaye da barna da shugabannin ke yi a Najeriya. Muna son mu fito da wasu hanyoyi da za su rage mana dogaro da mai, muna so mu kawo sauye sauye da za su nuna cewa shugabannin kasa bautar jama'a suke yi ba wai jama'a ne ke musu bauta ba. Sune muhimman maganganun da za a tattaunawa kansu a wannan taro."

To sai dai koma ya zuwa yaushe ne dai alamun nasarar 'yan sauyin ke iya baiyana gaban kowa ya gani dai, a tunanin Amina Mohammed da ke zaman daya a cikin sababbi na ministocin da ke shirin taka rawa a gwamnatin dai, taron na zaman dama ta fede biri ya zuwa wutsiya domin kowa ya tabbatar da abin da ke akwai a cikin hanjinsa.

Burin sabuwar gwamnatin Najeriya

"Wannan gwamnati za ta yi tunanin fitar da ajenda na canje-canjen da ya kamata a yi domin yakar cin hanci da karbar rashawa. Ajendar za ta bayyana irin canje canjen da ya kamata a yi ga dokoki da shi kansa kundin tsarin milkin kasar dan a aiwatar da abin da ake so a yi."

Abin jira a gani dai na zaman kamun ludayi na ministocin da suke shirin kama rantsuwar aiki a cikin makon gobe sannan kuma da kaiwa ga tabbatar da sauyin da kasar ke nema ido a rufe.