Najeriya: Buhari ya nada sabbin mukamai | Labarai | DW | 27.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: Buhari ya nada sabbin mukamai

Sabbin mukaman sun hada da sakataren gwamnatin tarayya da shugaban ma'aikata na fadar shugaban kasa da shugaban hukumar hana fasa kwauri ta kwastam da dai sauran wasu manyan mukamai.

Shugaban Muhammadu Buhari na Najeriya ya yi sabbin nade-nade na wasu manyan jami'an gwamnati a mukamai daban-daban. A cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar a yau, shugaban kasar ya nada Babachir David Lawal a matsayin sabon sakataren gwamnatin tarrayar kasar ta Najeriya yayin da kuma Alhaji Abba Kyari ya zamo shugaban ma'aikata na fadar shugaban kasa.

Ragowar sabbabin mukaman sun hada da Kanar Hamidu Ali mai ritaya da ya zamo sabon shugaban hukumar hana fasa kwauri ta kwastam, da kuma Kure Martins Abeshi wanda ya maye gurbin David Paradang a matsayin shugaban hukumar shigi da ficin kasar ta Immigration.

Shugaba Buhari har ila yau ya amince da nadin senata Ita Enang a matsayin mai ba shi shawara kan harkar majalisar dattawa, a yayin kuma da Hon Abdurahaman Kawu Sumaila ya zamo mashawarci a harkar majalisa ta wakilai.

Ana dai kallon sabbin nade-naden da suka zamo gamin gambizar 'yan siyasa da 'yan boko a matsayin alamu na irin alkiblar da gwamnatin ke shirin dauka mussaman ga batun yaki da hanci da rashawa cikin kasar: