Najeriya: Biyan bashin da wasu jihohin suka ci | Siyasa | DW | 18.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya: Biyan bashin da wasu jihohin suka ci

Alamu na nuna cewar gwamnatin Najeriya ba za ta baiwa jihohin kasar tallafin kudi kai tsaye don biyan bashi ba, maimakon hakan za ta biya musu basusukan da bankuna ke bin su da kanta.

Tun dai cikin watan jiya ne gwamnatin tarayyar Najeriya ta amince da sako kudi fiye da naira Bilyan 700 don tallafawa wasu jihohin Nigeriya da ke halin matsin tattalin arziki wanda ya kai wasunsu ga kasa biyan albashin ma'aikata ballantana gudanar da aiyyukan raya kasa. Salon bada wannan tallafin ya sauya don kuwa gwamnatin tarayya ta ce za ta biya bankuna ne kudaden da jihohin suka ciwo rance Allah bar shi jihohin su rika biyan gwamnatin tarayyar sannu a hankali har kusan shekaru 20 masu zuwa.

Nigeria Korruption

Masu yaki da cin hanci na ganin sabon salon biyawa jihohi bashi zai hana cin hanci

Masu sanya idanu kan lamuran yau da kullum a Najeriya da ma wasu al'ummar kasar na ganin cewar wannan matakin da gwamnatin ta dauka na kan hanya madaidaiciya domin kuwa wannan salon da ake zaton gwamnatin Muhammadu Buhari za ta yi amfani da shi zai taimaka wajen magance yin sama da fadi da wannan kudade domin kuwa jihohin ba su ma ga kudin ba balle su taba su.

To sai dai kuma wasu na gani wannan mataki zai kara janyo jihohin su kuma aukawa cikin matsin tattali kuma wasu jihohin zai kasance sun gagara yin aiyyukan raya kasa da suka kuduri aniyar yi idan tallafin ya samu. Tuni dai wasu jihohin Najeriya suka fara tattance maikatan bogi da nufin cike duk wani gibi na salwartar kudaden gwamnati don su samu damar yin amfani da kudade kan wasu abubuwan da suke son yi.

Nigeria Slum

Matsin tattalin arziki ya sanya jihohi da dama gaza yin aiyyukan raya kasa

Yayin da jihohin ke wannan aiki, wasu na cewar jihohin na yin hakan ne a wani mataki na jan kafa game da biyan albashi. Yanzu dai abin jira a gani shi ne yadda jihohin da wannan tarnaki na kudi ya shafa, za su wanye da matsalolin da ke gaban su duk kuwa da matakan tallafi da gwamnatin tarayya ta dauka don ceto su daga kangin bashin da suke ciki.

Sauti da bidiyo akan labarin