1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar bai wa matasa ilimin kimiyya

June 21, 2023

Shararren mai kudin nan na duniya wato Bill Gates ya bukaci gwamnatocin kasashe ma su tasowa da su mayar da hankali wajen bai wa matasa ilimi na zamani, musamman a fannin kimiyya da fasaha.

https://p.dw.com/p/4Su1Q
Bill Gates | Ilimi | Tallafi | Matasa | Najeriya
Shararren mai kudin duniya Bill GatesHoto: Lynch/MediaPunch/picture alliance

Shararren mai kudin na duniya Bill Gates ya yi wannan kiran ne a birnin Lagos da ke zaman cibiyar kasuwancin Najeriya, yayin wata ganawa da ya yi da matasa dangane da yunkurinsu nan zama da kafafunsu a fannin kasuwanci. Gates ya bayyana cewa, mayar da hankali wajen zuba jari a ilimin matasa zai taimaka gaya wajen cimma buri a fannin kimiyya da fasaha. Ya ce daukar nauyin ilimi shi ne babban abin da ke janyo ci-gaba a kasashe da dama. Shi dai Bill Gates ya jima yana gudanar da wata gidauniya da hadin gwiwar tsohuwar matasar Melinda wato "Bill & Melinda Gates Foundation", waddda ke taimakawa a kasashen Afirka da dama ciki har da Najeriya. Masana dai na ganin akwai tarin damarmaki a Najeriyar, abin da ya sanya mutane da dama daga kasashe makwabta kan shiga kasar domin neman abin dogaro da kai.