1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Banbanci kan talaka da mai kudi

Ahmed Salisu
October 9, 2018

Wani rahoto da kungiyar nan ta bada agaji ta Oxfam ta fidda ya nuna cewar Najeriya da Singapore da Indiya na kan gaba a kasashen da basa tabuka komai wajen kawar banbancin tsakanin talaka da mai kudi a kasashen.

https://p.dw.com/p/36Cdj
Symbolbild Südafrikas Wirtschaft -  Arbeitslosigkeit
Hoto: Imago

Rahoton na Oxfam ya ce a Najeriya alal misali, matasalar ta yi kamari ne saboda rashin maida hankali wajen karbar haraji yadda ya kamata da kuma yin aiyyukan da za su inganta rayuwar talaka, inda ya kara da cewar a Singapore ma dai matsalar irin ta Najeriya ce domin shafaffu da mai na kin biyan haraji.

To sai dai baya ga wadannan kasashe da rahoton ya ambato, ya kuma ce rashin daidaito a sauran kasashen duniya kai wani mataki mai daga hankali inda ya ce kashi daya na al'ummar duniya da ke da hannu da shuni ne ke juya kashi 4 cikin 5 na dukiyar da aka samu daga tsakiyar shekarar 2016 zuwa 2017.

Wannan ne ma ya sanya Oxfam din gargadin shugabannin duniya kan yiwuwar gaza cimma kudurin da aka dauka na samar da daidaito tsakanin al'umma daga nan zuwa shekarar 2030 inda ya yi kira garesu da su samar da hanyoyin da za a bi wajen cike wannan gibin.