1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Borno: Ta'azzarar hare hare lokacin azumi

May 6, 2019

Al'ummar shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya sun fara Azumi bana a yanayi na fargaba da kunci gami da yunwa sanadiyyar sabbin hare-haren da mayakan Boko Haram ke kaiwa a sassan Borno da Yobe

https://p.dw.com/p/3I1aC
Nigeria Ramadan Fastenbrechen in Sokoto
Hoto: DW/A. Abdullahi

Abinda ya sake jefa ayyukan jin kai cikin mawuyacin hali na matsalolin saboda sabbin ‘yan gudun hijira da ke samu a kullum.

Mayakan Boko Haram sun zafafa hare-hren da su ke kaiwa a sassan jihohin Borno da Yobe inda ko a karshen makon nan mayakan sun karbe iko da wani sansanin sojojin bayan harin da su ka kai tare da hallaka sojoji da dama.

Hare-haren sun jefa al'ummar yankunan cikin halin ni ‘ya su tare da tserewa daga garuruwan su domin tsira daga hare-haren a dai dai lokacin da aka fara azumin watan Ramadan na wannan shekara.

Lokacin shan ruwa na iyali
Lokacin shan ruwa na iyaliHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Maikatanga

Dubban ‘yan gudun hijira na kwarara Maiduguri da sauran yankuna saboda tsira daga hare-haren da kuma fada da ake gwabzawa a wasu yankunan Arewacin jihar Borno da kuma wasu bangarorin na jihar Yobe.

Yayin da ake suburbuda zafi da dama daga wadan ‘yangudun hijira na zube a sararin subaha inda wasu su ka samu karkashin bishiya su ka zauna wasu kuma sun hada kara da tsommukara sun samawa kan inuwar da za su shiga.

Mata da kananan yara su ne suka fi fama da matsalolin yunwa da na rashin wurin kwana inda yara da ba sa Azumin ba ma ba sa samun abinda za su ci inda tuni wasu su ka fara kamuwa da cutuka musamman saboda yadda zafin zana mai tsanani ke buga su saboda rashin matsuguni.

Yanayin shan ruwa a garin Sokoto
Yanayi shan ruwa a garin SokotoHoto: DW/A. Abdullahi

Kokarin jin ta baki hukumomin da kungiyoyin agaji da ke tallawa ‘yan gudun hijira ya ci tura.

Amma dai a kwanakin baya hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Borno tace tana samar da tallafi ga ‘yan gudun hijirar musamman sabbin zuwa sai dai da alamu abin baya wadar da su.

Yanzu haka dai masu hali da kuma wsu kungiyoyin na taimakawa ‘yan gudun hijirar da abinda za su ci a lokacin azumin sai dai kalilan ne kaiwa su ke samun irin wannan tallafi saboda yawan da ‘yan gudun hijirar ke ciki.