Najeriya: Atiku ya kara shan kayi a kotu | Labarai | DW | 30.10.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: Atiku ya kara shan kayi a kotu

A Najeriya, kotun koli ta yi watsi da karar da babbar jam'iyyar adawa ta kasar ta PDP ta daukaka a gabanta, tana mai kalubalantar zaben Shugaba Muhammadu Buhari.

A Najeriya, kotun kolin kasar ta yi watsi da karar da babbar jam'iyyar adawa ta kasar ta PDP ta daukaka a gabanta, tana mai kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa na ranar 23 watan Febuwarin da ya gabata, wanda dan takarar jam'iyyar APC Muhammadu Buhari ya lashe da kaso 56 daga cikin dari a yayin da abokin hamayyar tasa Atiku Abubakar ya samu kaso 41 daga cikin dari.

 Babban alkalin kotun Tanko Muhammad ne ya bayyana wannan hukunci a wannan Laraba inda ya ce, sun yi watsi da karar ne domin kuwa zarge-zargen da hujjojin da jam'iyyar adawar ta gabatar ba su gamsar da kotun ba. Amma ya ce sai a nan gaba ne kotun za ta bayyana dalillan da suka sa illahirin alkalai bakwai na kotun suka yi watsi da karar jam'iyyar adawar.

 Dama dai a tsakiyar watan Satumban da ya gabata, a matakin farko na shari'a, kotu ta yi watsi da karar da dan takararar adawar Atiku Abubakar ya shigar a gabanta domin neman a soke sakamakon zaben. Da wannan hukunci dai, kotun ta kawo karshen rikicin sakamakon zaben wanda aka share watanni takwas ana yi tsakanin manyan jam'iyyu biyu na Najeriyar a gaban kuliya.