1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kubutar da 'yan makarantar Islamiyya

Ramatu Garba Baba
October 15, 2019

Yara da matasa na daga cikin mutum 70 da rundunar 'yan sanda a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya ta yi nasarar kubutarwa daga wata makarantar Islamiyya ta gyara halinka a garin Daura.

https://p.dw.com/p/3RI9o
Nigeria Polizei befreit Koranschüler aus unmenschlichen Bedingungen
Hoto: Reuters/Str

'Yan sandan jihar ne suka kai samame makarantar,  inda suka yi nasarar kubuto da mutanen masu shekaru tsakanin bakwai zuwa arba'in, an tadda wasunsu garkame da ankwa da wasu sarkoki. Kakakin 'yan sandan jihar Sanusi Buba, ya ce bayan bincike da suka gudanar, daga cikin yaran sun fada musu yadda ake gallaza musu azaba.

Wannan samamen na jihar Katsina na zuwa ne kwanaki bayan wani da aka kai a jihar Kaduna, inda nan ma aka gano yaran da aka kai makarantar Islamiyyan da sunan karatu amma suka tsinci kansu cikin wani yanayi na kunci a sakamakon azabar da malamai ke gallaza musu da sunan gyara musu tarbiyya.