Najeriya: An kama shugaban hukumar EFCC | Labarai | DW | 06.07.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: An kama shugaban hukumar EFCC

Jami'an tsaro a Najeriya sun gayyaci  shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC Malam Ibrahim Magu domin yi masa tambayoyi.

Bayanai daga a Abuja babban birnin kasar Najeriya na nuni da cewa jami'an tsaro sun isa a ofishin hukumar EFCC Malam Ibrahim Magu inda suka bukaci shugaban ya tafi tare da su.

A sanarwar da hukumar tsaro ta farin kaya ta DSS ta fitar wacce jami'in yada labaru na hukumar Peter Afunanyan ya sanya hannu kanta, ta ce bata kame shugaban na EFCC, amma bayanai sun nuna cewa yana hannun jami'an tsaron na Najeriya.

Sai dai bayyanai sun nuna cewa shugaban hukumar ta EFCC mai yaki da yiwa tattalin arzikin kasar zagon kasa Malam Ibrahim Magu, na fuskantar zarge-zarge na cin hanci da rashawa a kasar.