1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Cinkin jarirai a yankin kudanci

Abdourahamane Hassane
June 16, 2022

Yan sanda a Najeriya sun kubutar da wasu ‘yan mata matasa 35 a wani otel da ke kudu maso gabashin kasar, inda wasu ‘yan fashi suka tilasta musu yin karuwanci, domin haifar ‘ya'ya da ake sayar da su,

https://p.dw.com/p/4CpOM
Menschenhandel in Nigeria
Hoto: picture-alliance/Ton Koene

An ceto 'yan mata masu shekaru 14 zuwa 17 a otel din gally-gally da ke a jihar Anambra inda ake yin amfani da su a matsayin bayi domin yin karuwanci don haifar da jarirai. A halin da ake ciki hudu daga cikin 'yan matan na da ciki, 'yan sanda sun ce sun gano makamai da kudade. Kawo yanzu an kama wasu mutane guda uku yayin da mai otel din ya ramta cikin na kare. Fataucin matan da kanana yara wani abu ne da ya zama ruwan dare a yankin kudu maso gabashin Najeriya duk da kokarin da gwamnatin ke yi na shawo kan matsalar.