1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An maye girbin SARS da rundunar SWAT

October 13, 2020

Babban sufeton 'yan sandan Najeria Mohammed Adamu ya sanar da kafa sabuwar rundanar tsaro da zata maye gurbin SARS mai yaki da fashi da makami.

https://p.dw.com/p/3jtBd
Nigeria Sicherheitskräfte Kampf gegen Boko Haram
Hoto: Getty Images/AFP/Q. Leboucher

Kasa da mako guda da soke rundunar 'yan sanda mai yaki da fashi da makami SARS, babban sufeton 'yan sanda na Najeriya Mohammed Adamu ya bayar da sanarwar maye gurbin ta da wata rundunar da za ta yi yaki da bazuwar muggan makamai SWAT wato Special Weapons and Tactics a turance.

Cin zarafin da tsohuwar rundunar ta SARS ta jima tana yi wa jama'a a kasar, ya harzuka dandazon matasa musamman a kudacin kasar da ma kungiyoyin kare hakkin bil adama na ciki da wajen kasar mamaye manyan titunan wasu birane inda suka bukaci da a kawo karshen rundunar.

A ranar Lahadin da ta gabata ce babban sufeton ya sanar da rushe rundunar ta SARS bisa umurnin shugaban kasar Muhammadu Buhari.