1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Kundi ajiye sunayen masu ci zarafin mata

Binta Aliyu Zurmi
November 25, 2019

A Najeriya a karon farko an kaddamar da wani kundi na ajiye sunayen mutanen da suka aikata laifin cin zarafin mata ta hanyar lalata. 

https://p.dw.com/p/3Thg0
Nigeria Lagos | Schwangere Frau wurde von Polizei befreit
Hoto: Reuters TV

Kundin zai kunshi sunayen dukkan wadanda aka taba zartar da hukunci a kansu bisa laifin yin lalata ta hanyoyi dabam-dabam, a wannan kasa da ke mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka. Za'a iya samun wannan kundi ta yanar gizo, domin taimaka wa al'umma da kungiyoyi da hukumomin jiha da kuma na 'yan sanda gudanar da bincike kan wadanda ka iya maimaita aikata irin wadannan laifuka.