1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Najeriya: An dakatar da yajin aikin masu dakon mai

October 11, 2021

Bayan sanarwar fara yajin aiki na kasa baki daya, direbobin manyan motocin dakon mai a Najeriya sun sasanta da mahukunta. Yanzu dai suna aiki yadda aka saba.

https://p.dw.com/p/41Vai
Nigeria Tankstelle in Lagos
Hoto: AFP/Getty Images/E. Arewa

Kungiyar direbobin dakon mai a Najeriya, ta dakatar da yajin aiki na kasa baki daya da ta shirya farawa a wannan Litinin.

Kungiyar ta ce ta dakatar da yajin aikin ne bayan ganawa da kamfanin mai na kasa NNPC a jiya Lahadi, da kuma wani zaman da za a yi a ranar Talata 12 ga watan Oktoba.

Dakatar da yajin aikin dai ya zo ne bayan NNPCn ya nuna damuwa da irin halin da 'yan Najeriya ke iya shiga na karancin mai muddin direbobin suka fara yajin aikin.

Kungiyar direbobin dakon mai wato NUPENG ta shirya yajin aikin ne saboda bukatar hukumomi su dauki matakan gyara hanyoyin kasar da ta ce hadari ne babba ga rayuwar direbobi a Najeriyar.