1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: AMCON ta karbe iko da kamfanin Arik Air

Uwais Abubakar Idris | Salissou Boukari
February 10, 2017

Sanarwar karbe ikon gudanarwar na kamfanin sufurin jiragen sama na Arik Air da hukumar ceto kadarori ta Najeriya AMCON ta yi domin ceto kamfanin ya sanya maida martani da ma duba tasirin yin hakan.

https://p.dw.com/p/2XKc7
Großbritannien Flugzeug von Arik Air landet in Heathrow
Hoto: Imago

Daukan wannan mataki da hukumar ta AMCON ta yi a kan kamfanin jiragen saman na Arik dai ya biyo bayan tabarbarewar gudanar da harkokinsa saboda matsaloli na dimbin bashi na milyoyi da kamfanin ke fama da shi, domin mafi yawan jiragen nasa basa iya kai-da-komowa abinda ya sanya a fili ake ganin ya kama hanyar durkushewa. Yawaitar jinkiri da soke jiragen saman bayan sun sayar da tikiti na zaman na kullum, abinda ya sanya Gwamnatin Najeriyar a karkashin hukumar Amcon bayyana cewa manufar karbe ikon gudanar da kamfanin ita ce ta kai dauki don ceto shi.

Harold Olusegun Demuren
Harold Olusegun Demuren Shugaban kamfanin Arik Air Hoto: AP

Irin hali na rashin tabbas da wannan muhimmin sashe na sufurin jiragen sama ya shiga a Najeriya, kuma indan aka fara lissafi na kamfanonin da suka  dukushe su na da yawan gaske kuma abun da ke da tayar da hankali ga makomar sashen da ke da muhimmancin gaske ga 'yan Najeriya da ma makwabtanta. Ga 'yan Najeriya da suke cikin dandana azabar jinkiri da ma yawan soke jiragen bayan sun sayi tikiti sun karbi wannan mataki da hannu biyu-biyu inda suke fatan ganin wannan mataki zai iya kawo karshen tarin matsalolin da suke fuskanta tare da wannan kamfani.

Wannan dai shi ne kamfanin jiragen sama na uku da hukumar da ke coto kamfanoni a Najeriya ta AMCON ta karbe ikon gudanar da shi baya ga Aero da Afrijet. Abin jira a ganin dai shi ne mataki na gaba da kamfanin na Arik zai dauka saboda nuna adawa da wannan mataki da ya ce zai kalubalanci lamarin, a yayin da ake fatan wannan zai iya taimakawa wajen ceto harakar ganin cewa kamfanin na Arik ne ke da kusan kaso 60 cikin 100 na zirga-zirga sufurin jiragen saman Najeriyar.