1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar tsagaita wuta ta kankama a arewacin Siriya

Abdoulaye Mamane Amadou MNA
October 21, 2019

Rahotanni daga birnin Ras al-Aïn a arewacin Siriya sun tabbatar da janyewar dakarun sojan Siriya da galibinsu Kurdawa ne daga yankin inda sojojin Turkiyya suka ja daga.

https://p.dw.com/p/3Rbno
Syrien l Militäroffensive der Türkei in der Grenzstadt Tel Abyad
Hoto: Reuters/K. Ashawi

Tun a ranar Assabar ne shugaban rundunar FDS Mazloum Abdi ya tabbatar da cewa sojan za su karkare ficewa daga yankin, muddin Turkiyya ta tabbatar da dakatar da luguden wutar da take yi, kamar yadda yarjejeniyar tsagaita wuta da kasar Amirka ta cimma da hukumomin Turkiyya ta shata.

Ita ma dai ma'aikatar tsaron kasar Turkiyya ta tabbatar da ficewar sojojin inda ta ce wani ayarin motocinta dauke da muggan makaman yaki 55 sun dira a yankin, a yayin da wasu 86 na dakarun Kurdawan suka fice inda suka nufi yankin Tal Tamr.

A yayin wani sakonsa da ya wallafa a shafin Twitter a yau din nan Shugaban Amirka Donald Trump ya ce yarjejeniyar da bangarorin suka cimma ta tsagaita wuta tana nan daram.