Mutane sama da 80 sun hallaka a Indiya | Labarai | DW | 12.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane sama da 80 sun hallaka a Indiya

Wannan adadi ya ma karu bisa bayanan da ke kafofin yada labarai, kuma hakan ya faru ne bayan da wata tukunyar gas ta fashe.

Mutane sama da tamanin ne suka halaka bayan da wata tukunyar gas ta fashe a wani shagon cin abinci abin kuma da ya shafi makwabtansa a tsakiyar jihar Madhya Pradesh ta kasar Indiya kamar yadda wani babban jami'in lafiya ya bayyana a ranar Asabar din nan. Wannan adadi dai ya karu cikin sauri bayan tun da fari aka ce mutane 20 ne abin ya ritsa da su amma daga bisani aka gano wasu da ke binne cikin baraguzai na ginin da ya lalace sakamakon fashewar da ma ta hada wasu gine-gine makwabtan shagon a garin Petlawad a lardin Jhabua.

A cewar Arun Kumar Sharma, babban jami'in lafiya a lardin na Petlawad a zantawarsa da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP baya ga mutanen sama da 80 da suka rasu akwai kuma kimanin 100 da suka samu raunika.

Wannan katafaren shagon cin abinci dai ya kasance matattara ga ma'aikata da yara 'yan makaranta inda suke taruwa dan yin karin kumallo kuma hadarin ya faru ne da misalin karfe takwas da rabi agogon kasar ta Indiya a cewar Seema Alava babban jami'in 'yan sanda a yankin.