1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane da dama sun rasu a wani mummunan faɗa a lardin Waziristan

October 7, 2007
https://p.dw.com/p/Bu93
Rundunar sojin Pakistan ta ce an kashe wasu ´yan takife kimanin 50 da kuma sojoji 20 a wani kazamin fada da aka gwabza a yankin arewa maso yammacin kasar. Rundunar ta ce an gwabza fadan ne a lardin arewacin Waziristan mai kwarya-kwaryar ´yancin cin gashin kai bayan da ´yan tawaye suka kai harin kan wani ayarin motocin soji. Wannan yanki dai dake kan iyaka da Afghanistan na zama wani sansani na magoya bayan kungiyar Taliban da ´yan ta´addan kungiyar al-Qaida.