Mutane da dama sun rasa rayukansu a birnin Najaf | Labarai | DW | 10.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane da dama sun rasa rayukansu a birnin Najaf

Wani bomb da ya fashe a wata kasuwar dake birnin Najaf na kudancin Iraqi, ya yi sanadiyar mutuwan mutane 30 yayinda wasu 50 suka ji rauni. Rahotanni sunce wani dan harin kunnar bakin wake ne ya kai harin dai dai wani wurin bincike da yan sanda suka kafa, kusa da wajen ibadan yan shi’a na Imam Ali. Najaf wani birni ne inda mabiya darikar shi’a suka fi runjaye, mai nisan kilo mita 160 daka babban birnin Iraqi. Birnin Najaf ya zama wani dandali na kai hare hare da zubar da jinni tun lokacin da Amurka ta mamaye Iraqi a shekarar 2003.