Mutane aƙalla 35 suka mutu a birnin Mosko a sakamakon tashin bam | Labarai | DW | 29.03.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane aƙalla 35 suka mutu a birnin Mosko a sakamakon tashin bam

Hare haren bama bamai guda biyu a tashoshin jiragen ƙasa na birnin Mosko na ƙasar Rasha sun kashe mutane 35

default

Dan Sanda a tsakiyar birnin Mosko

A ƙasar Rasha an bada rahoton tashin wasu bama bamai a tashoshin jiragen ƙasa na Mosko babban birnin kasar inda suka kashe a ƙalla mutane 35.

Tun da farko dai bam din ta tashine a tashar jiragen kasa ta loubianka dake tsakiyar Mosko ta kashe mutane 20 tare da raunata wasu 11,kafin daga bisani wata bam din ta biyu ta tashi a tashar park Koultouri inda ta kashe mutane da dama ,wanda haryanzu kanfanin dilanci labarai na kasar ta Rasha na ria da interfax suka ce ba a da yawan adadin mutane da suka mutu. Sanan rahotani na baya bayanan da aka samu sun nuna cewa matne su kai hare hare na ta'danci.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane

Edita : Abdulahi Tanko Bala