Mutane aƙalla 35 suka mutu a birnin Mosko a sakamakon tashin bam
March 29, 2010Talla
A ƙasar Rasha an bada rahoton tashin wasu bama bamai a tashoshin jiragen ƙasa na Mosko babban birnin kasar inda suka kashe a ƙalla mutane 35.
Tun da farko dai bam din ta tashine a tashar jiragen kasa ta loubianka dake tsakiyar Mosko ta kashe mutane 20 tare da raunata wasu 11,kafin daga bisani wata bam din ta biyu ta tashi a tashar park Koultouri inda ta kashe mutane da dama ,wanda haryanzu kanfanin dilanci labarai na kasar ta Rasha na ria da interfax suka ce ba a da yawan adadin mutane da suka mutu. Sanan rahotani na baya bayanan da aka samu sun nuna cewa matne su kai hare hare na ta'danci.
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Abdulahi Tanko Bala