Mutane 44 sun rasu a hadarin wani jirgin saman sojin Slovakiya | Labarai | DW | 20.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 44 sun rasu a hadarin wani jirgin saman sojin Slovakiya

´Yan sandan kasar Hungary sun ce mutane 44 sun rasu yayin da mutum daya ya tsallake rijiya da baya a wani hadarin jirgin saman sojin kasar Slovakiya da ya auku a kusa da iyakar kasasshen biyu. Jirgin saman wanda ke dauke da dakarun Slovakiya da ke aiki karkashin rundunar kiyaye zaman lafiya ta KFOR, yana kan hanyar sa ne daga lardin Kosovo zuwa Slovakiya lokacin da hadarin ya auku a kusa da kan iyakar kasar. Jami´an Hungary sun ce har yanzu ba´a gano musababbin faduwar jirgin saman ba, ko da yake kafofin yada labaru sun ce jirgin ya kama da wuta kafin ya fadi a wani yanki mai tsaunuka.