Mutane 20 sun mutu a farmakin Kamaru | Labarai | DW | 26.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 20 sun mutu a farmakin Kamaru

Lokacin da waɗanda ba su sami raunika ba suka bi maharin sai ya riƙa jefa musu makaman gurneti abin da ya sanya ya gudu.

Kamerun Anschlag in Maroua

Bayan kai farmaki a Maroua

Aƙalla mutane 20 ne a ke saran sun mutu bayan wani farmakin bam a wata mashaya daren Asabar a birnin Maroua da ke Arewacin Kamaru kamar yadda wata majiyar tsaro ta tabbatar wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP.Wannan farmaki dai na zama na biyu a yankin bayan hari da aka kai a ranar Laraba da yayi sanadin kisan mutane 13 a wasu tagwayen hare-haren bama-bamai da aka yi amfani da wasu ƙananan yara 'yan mata wajen kai shi.

A cewar wani soja da ke aikin yaƙi da mayaƙan Boko Haram da bai so a bayyana sunansa ba ya ce da misalin karfe 9:30 ne agogon ƙasar takwas da rabi agogon GMT aka kai wannan farmaki . A cewar majiyar jami'an gwamnati akwai mutane da dama da suka sami raunika a wannan hari.Wasu da suka ga yadda lamarin ya afku a lardin na Ponre sun bayyana cewar maharin ya jefa bama-baman ne a mashayar sannan ya ruga a guje lokacin da wadanda ba su sami raunika ba suka bi shi sai ya riƙa jefa musu makaman gurneti abin da ya sanya ya gudu.

A ranar Laraba ma a tagwayen hare-haren da aka kai babbar kasuwa da yankin da ke kusa mutane 13 ne suka rasu.