Mutane 16 sun rasa ransu sakamakon hadarin motocin safa a Rasha | Labarai | DW | 05.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 16 sun rasa ransu sakamakon hadarin motocin safa a Rasha

Hukumomin sun tura motocin daukan marasa lafiya da jiragen sama maus saukan ungulu domin kwashe mutane a wajen da aka yi hadarin

Mutane 16 sun hallaka yayin da wasu fiye da 50 suka samu raunika, lokacin da manyan motocin safa suka yi taho mu gama a yankin gabashin kasar Rasha. Ma'aikatar lafiya ta ce 10 daga cikin wadanda suka samu raunika suna cikin matsananci hali.

An tura motocin daukan marasa lafiya da jiragen sama masu saukan ungulu domin kwashe wadanda suka samu raunika. Kimanin mutane dubu-27 ke mutuwa duk shekara sakamakon hadarin a kan hanyoyin kasar ta Rasha.