Mutane 13 ′yan kasar wajen sun mutu a harin Afghanistan | Labarai | DW | 18.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 13 'yan kasar wajen sun mutu a harin Afghanistan

Daga cikin mutane 21 da suka rasu sakamakon harin da aka kai wani gidan cin abinci a birnin Kabul a jiya, 13 daga ciki 'yan kasashen ketare ne.

Biyu daga cikin mutanen Amirkawa ne, biyu 'yan Birtaniya da wani jami'in bankin bada lamuni na duniya dan asalin kasar Lebanon, sai kuma mai gidan abincin wanda shi ma dan Lebanon din ne.

Sauran sun hada da wani dan kasar Denmark da ke aiki da rundunar 'yan sanda ta kungiyar Tarayyar Turai ta EU da kuma wani jami'in Majalisar Dinkin Duniya dan asalin kasar Rasha.

Tuni dai kasashen duniya da mahukuntan na Afghanistan suka nuna takaicinsu dangane da wannan hari na jiya, inda shugaba Hamid Karzai na Afghanistan din ya kira ga dakarun kawance na NATO da su matsa lamba wajen yakar ta'addaci a kasar.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman