Museveni na kan gaba a sakamakon zaben Yuganda | Labarai | DW | 15.01.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Museveni na kan gaba a sakamakon zaben Yuganda

Hukumar zabe ta kasar Yuganda ta sanar da cewa shugaban kasar Yoweri Museveni na kan gaba a zaben shugabancin kasar da aka gudanar.

Hukumar ta ce sakamakon da aka samu ya zuwa yanzu na kashi 29 cikin dari na mazabu ya nuna Museveni ya sami kashi 63 cikin dari, yayin da abokin hamaiyarsa  Bobi Wine ya sami kashi 28 cikin dari na yawan kuri'un da aka kada.

Birnin Kampala da aka sami da hada-hada a yau Juma'a ya kasance shiru. Zaben dai ya ci karo dirar mikiya na jami'an tsaro akan yan takarar adawa da magoya bayansu.

Bobi Wine mawakin da ya rikide ya koma dan siyasa ya zaburar da matasan Yuganda tare da kiran kawo sauyi. Yace jamian tsaro sun firgita ma'aikatan zabe ya kuma yi watsi da sakamakon wanda yace yana cike da kura kurai da kuma magudi.

Amirka da kungiyar tarayyar Turai da Majalisar Dinkin Duniya da kuma kungiyoyin farar hula duk sun baiyana damuwa akan ingancin zaben. Kungiyar tarayyar Afirka AU ita ce kadai ta tura jami'an sa ido kan zabe tare da kungiyar mata ta kungiyar AU.