Murar kaji a kasar Turkiyya | Zamantakewa | DW | 09.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Murar kaji a kasar Turkiyya

A hankali dai murar kaji na ta kwararowa zuwa yammacin Turai. Mutuwar mutane biyu da aka jibinta ta da kamuwarsu da cutar a kasar Turkiyya na janyo damuwa ga jami'an kiwon lafiya a kasashen yammacin Turai.

Daukan matakan riga kafi; fesa wa motoci magungunan kashe kwayoyin cutar a Turkiyya.

Daukan matakan riga kafi; fesa wa motoci magungunan kashe kwayoyin cutar a Turkiyya.

A kasashen yammacin Turai dai, ana ta fargabar kwararowar cutar nan ta murar kaji. Tun da aka sami labarin barkewar cutar a gabashin Turkiyya da kuma tsakiyar jihar Anatoliya ta kasar ne jami’an kiwon lafiya a yammacin Turai suka dinga nuna damuwarsu. A kewayen birnin Ankara kuma, wato babban birnin kasar, an tabbatar cewa, mutane 3 sun kamu da cutar. Kawo yanzu dai, kusan mutane 15 ne ake zaton sun kamu da cutar, wadda ta janyo sanadiyar mutuwar yara biyu a makon da ya gabata. Kafin dai a ga alamun cutar a jikin mutane, sai da aka fara gano hakan a binciken da aka gudanar kan dabbobin kiwo, wadanda su ma ake zaton sun sami cudanya ne da tsuntsaye. A halin yannzu dai, likitoci a asibitin birnin Ankara na kira ne ga jama’a da su yi taka tsantsan wajen kulawa da dabbobinsu, musamman ma dai masu fukafukai. Kamar yadda babban likitan asibitin Numune na birnin ya bayyanar game da wani mutumin da aka kawo nan kame da cutar:-

„An kawo mana wani maras lafiya, mai suna Mustafa Cankar, mai shekaru 60 da haihuwa. Mun kwantad da shi a asibitin ne, bayan da muka ga cewa yana dauke da kwayoyin cutar. Amma a halin yanzu, yana samun sauki. Muna ganin cewa, ya kamu da kwayoyin cutar ne bayan da ya yanka kaza a gonarsa.“

Har ila yau dai, ba a tabbatar da yaduwar cutar tsakanin mutane ba. Ta cudanya da dabbobi masu fukafukai ne mutum ke iya kamuwa da kwayoyin wannan cutar. A kasar Turkiyyan a halin yanzu, kusan mutane 30 ke kwance a asibitoci saboda tabbatad da kamuwarsu da kwayoyin cutar da aka yi. Abin damuwa dai shi ne ganowar da aka yi ta cewa, cutar ta yadu zuwa jihohi 10 daga jihohi 81 na kasar, wadanda suka hada da arewaci da kuma yammacin kasar, inda aka fi samun yawan masu yawon shakatawa.

Tuni dai kasashen da ke makwabtaka da Turkiyyan sun fdara daukan matakan riga kafi don shawo kan yaduwar cutar zuwa yankunansu. A lal misali, Rasha ta gargadi `yan kasarta da su guji kai ziyara a Turkiyya a halin yanzu. Kazalika kuma, Iran ta ce ba za ta bari manyan motoci su shigo kasar daga Turkiyya ba, sai an fesa musu magungunan kashe kwayoyin cutar.

Ministan noma na Turkiyyan, Eker, ya umarci duk masu kiwon kaji da ka da su bar su su fito daga akurkinsu. Kuma duk kajin da za a samu da alamun kamuwa da kwayoyin cutar, nan take ne ya kamata a kashe su, ko kuma a ke be su daga sauran dabbobin da ake kiwonsu. Ma’aikatar ta kuma sanya takunkumin hana farauta na wucin gadi a wasu yankunan. Ta kuma ba da lambobin wayar tarho, inda jama’a za su iya bugawa su sami karin bayani a kan matakan riga kafin da za su iya dauka game da cutar. Bugu da kari kuma, ana ta rarraba takardun da aka buga bayanai a kansu ga jama’a, sa’annan duk kafofin ya da labaran kasar na nasu iyakacin ko karin wajen fa dakad da jama’a.