Mumunar gobara a birnin London | Labarai | DW | 14.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mumunar gobara a birnin London

Wata mumunar gobara cikin daren Talata a London, ta mamaye wani bene dauke da gidaje masu yawa da ya zuwa yanzu, ba a tantance musabbabinta ba. Tuni dai hukumomi suka bayyana lamarin da wani babban bala'i.

Akalla jami'an kwana-kwana 200 ke kokarin shawo kan gobarar da ta kama wani dogon benen da ke yammacin birnin na London inda mutane da dama suka makale. Gobarar da ta fara ne kusan karfe daya na dare agogon GMT, ta kuma mamaye ilahirin katafaren ginin ne mai hawa 27 inda mutane da dama ke barci a cikinsa. Ko a safiyar wannan Larabar ma dai wasu hotuna sun nonu irin ta'asar da wutar ke yi.

Shaidu sun ce sun yi ta jin yadda mutane ke kururuwar kiran kai masu dauki cikin ginin wanda ke dauke da gidaje sama da 120. An dai yi nasarar ceto mutane, inda ake yi wa wasu kimanin 30 maganin a wasu asibitoci. Wutar wadda ta kazanta matuka, ka iya lakume kafatanin ginin da ke a North Kensington da ke a yammacin birnin na London. Ba a dai tantance musabbabin tashin wutar ba, ya zuwa yanzu.