Namadi Sambo dan siyasa ne dan asalin jihar Kaduna wanda ya mulki jihar a matsayin gwamna. Gabannin shigarsa siyasa, Namadi dan kasuwa ne.
A shekarar 2010 ne ya hau kujerar mataimakin shugaban kasa bayan da aka rantsar da Goodluck Jonathan a matsayin shugaban kasa, biyo bayan rasuwar Umaru Musa 'Yar Aduwa.