An kawo ci-gaba inji Namadi Sambo | Siyasa | DW | 18.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An kawo ci-gaba inji Namadi Sambo

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce ta yi rawar gani a kokarin sake farfado da harkokin wutar lantarki da sufuri.

AUSSCHNITT AUS: Nigeria's Vice President Namadi Sambo (R) and Deputy President of the Senate Ike Ekweremadu stand for the national anthem during the national inter-denominational funeral rites of Nigeria's secessionist leader Odumegwu Ojukwu at Michael Opkara Square in Enugu, southeastern Nigeria, on March 1, 2012. Soldiers fired a 21-gun salute at the funeral of Odumegwu Ojukwu on Thursday as Nigerian leaders paid final respects to the man whose 1967 declaration of Biafran independence sparked a civil war. Forty-five years after he tried to split Nigeria asunder by proclaiming the Republic of Biafra, Ojukwu's coffin was draped in the national colours of white and green at the funeral service in the city of Enugu, attended by thousands. Ojukwu died in November in Britain at the age of 78 but his body was only flown back on Monday. AFP PHOTO/ PIUS UTOMI EKPEI (Photo credit should read PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images)

Namadi Sambo

Ya zuwa badi dai a cewar mataimakin shugaban kasar Namadi Sambo kuma jagoran samar da wutar kasar. 'Yan Najeriya suna shirin ganin daban a cikin harkokin wutar da suka share shekara da shekaru suna fatan kawo karshen matsalar, amma kuma suka kare ba tare da samun ci -gaba ba. Akalla megawatt 9000 ne dai a cewar Arc Namadi Sambo, tarayyar ta Najeriya ke shirin samu a badin, abun kuma da a cewar sa ya kama hanyar kaddamar da kasar cikin tarihin kawo karshen matsalar da ake ta'allakawa da koma bayan kasar na lokaci mai tsawo.

Neue Umgehungsstraßen in Katsina, Nordnigeria. Die Straßenlaternen werden mit Solarenergie betrieben. Foto: DW/Thomas Mösch, 6.4.2011, Katsina / Nigeria

Wutan lantarki ta hasken rana a Katsina

Tuni dai Tarayyar Najeriyar a cewar mataimakin shugaban ta kai ga cefanar da daukacin cibiyoyin samar da wutar kasar, sannan kuma ta na shirin amfani da kudin wajen sake ginin wasu sababbi na ruwan saman da za su baiwa kasar karin megawatt 5000 cikin wasu shekaru biyar masu zuwa.

Babbar takadama cikin kasar ta Najeriya ya zuwa yanzu dai na zaman na tsadar ayyukan kwangilar sababbin cibiyoyin wutar kasar da kafafen yada labarai, suka ce na zaman mafi tsada a duniya amma kuma Sambo ya kira zuki ta Malle.

A Turkish Airlines passenger aircraft prepares to land at Heathrow Airport in west London on December 22, 2010. The race was on at snowbound European airports Wednesday to clear the backlog of stranded passengers in time for Christmas as weather conditions eased slightly. Thousands of weary passengers woke up in airport terminals around the continent, where stranded travellers have been bedding down since Friday, still in the hope of making it to their destination before Christmas Day on Saturday. AFP PHOTO /CARL COURT (Photo credit should read Carl Court/AFP/Getty Images)

Jirgin saman Turkish Airlines

Ko bayan batun wutar da ya gagari kundila dai, a cewar mataimakin shugaban Najeriyan, lokaci ya iso na tsalen murna a bangaren al'umar arewacin kasar, da a baya suka sha korafin nuna wariya wajen gina filayen jiragen saman kasar.

Ya zuwa yanzu dai gwamnatin da ta ce tana shirin kara fadin filin jirgin saman Aminu Kano da ke birnin Kano, ta kuma ce ta bar izini ga jiragen sama na Emirate Airline na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Turkish Airline na Turkiya za su fara sauka da tashi daga birnin Kano dama filin jirgin sama na Abuja.

An dai share tsawon lokaci ana kace-nace a tsakanin gwamnatin kasar da yar uwarta da ke jihar Kano game da batun hanawa manyan jirage na duniya zuwa Kano dama sauran sassa na arewacin Najeriya.

Mawallafi: Ubale Musa

Edita: Usman Shehu Usman

Sauti da bidiyo akan labarin