MOD.: HARKOKIN SIYASA A KASAR IRAQI. | Siyasa | DW | 19.02.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

MOD.: HARKOKIN SIYASA A KASAR IRAQI.

A yayin da harkokin siyasa suka dauki zafi a kasar Iraqi dangane da bukatar gudanar da zabe daga bangaren yan kasar,a yau alhamis sakataren Mdd Kofi Anan ya tabbatar da cewa zabe na mika mulki hannun yan kasar ta Iraqi da kasar Amurka ta kuduri aniyar yi a ranar 30 ga watzan juni ba zai taba yiwuwa ba.
Daukar wan nan mataki a cewa Anan ya faru ne bisa irin halin yanayin da kasar ke ciki a halin yanzu na rashin zaman lafiya.A don haka Anan ya kara da cewa gudanar da zabe a kasar ta iraqi na bukatar karin lokaci na yin shiri cikin tsanaki don kada gaggawa tazo ta haifar da dan da bashi da ido a nan gaba.
Kofi Anan yaci gaba da fadawa yan jaridun cewa bisa wadan nan dalilai na sama yana ganin akwai alamun cewa mutanen kasar ta iraqi zasu fahinci abin da yake son su gane dangane da gudanar da zaben na ranar 30 ga watan junin na wan nan shekara da muke ciki.
Bugu da kara sakataren na mdd ya tabbatar da cewa as nan gaba kadan wakilai daga majalisar ta dd zasu zauna don yin nazari na lokacin daya dace a gudanar da wan nan zabe na mikawa yan kasar ta iraqi mulkin su a hannun su.
A karshe Anan yayi alkawarin ganin cewa a nan gaba hukumarsa tayi aiki tukuru kafada da kafada ta da kasar Amurka da kuma yan kasar ta iraqi wajen tabbatar da wanzuwar mulki na dimokradiyya tare da taimakawa wajen farfado da tattalin arzikin kasar,muddin dai harkokin tsaro a kasar suka inganta.
A hannu daya kuma kafin wadan nan kalamai na Anan a can baya masu nazarin siyasa na mdd sun shaidar da cewa gudanar da zabe a kasar ta iraqi a halin yanzu abune da zai kara dagula al,amurra na siyasa a cikin kasar a nan gaba musanmamma bisa la,akari da rashin harkokin tsaro dake gudana a cikin kasar.
Bisa kuwa rahotanni da suka iso mana daga kasar ta iraqi wan nan bayani na soke zaben ranar 30 ga watan yunin ba zaiwa da dama daga cikin yan kabilar shi,a dadi ba bisa hujjar cewa sune a kann gaba dake muradin ganin an gaggauta yin zaben don mika musu mulkin su a hannun su.
Kafin dai kiraye kirayen da yan kabilar ta shi,a suka dinga yi na gudanar da zaben a can baya shugaban kabilar ta shi,awan a iraqi wato Ayatolla Ali Al sistani ya nuna rashin amincewar magoya bayan darikar tasa na gudanar da zaben gunduma gunduma da Amurka tayi shirin yi a kasar da cewa kamata yayi ayi zabe na gama gari don zabar wadanda suka cancanci su mulki kasar a nan gaba.
A waje daya kuma wata majiya mai karfi daga kasar ta iraqi ta shaidar da cewa idan zabe yaki yiwuwa a kasar bisa ire iren dalilan da Kofi Anan ya habarta a ´baya to hanya daya kawai da za,a warware al,amurra itace ta gudanar da zabe a yankuna yankuna a maimakon na gaba daya ,ko kuma a zabo wakilai daga bangarorin kasar daban daban a mika musu mulkin a hannun su.
To amma kuma hakan a cewar majiyar akwai shakku na samun yardar magoya bayan darikar shi,a game da wadan nan matakai biyu,a don haka ya zama wajibi a jira abin da mdd zata yanke a nan gaba game da matakin daya kamata a dauka a nan gaba dangane da gudanar da zaben na gaba daya a kasar ta iraqi.

 • Kwanan wata 19.02.2004
 • Mawallafi Ibrahim Sani.
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Bvlm
 • Kwanan wata 19.02.2004
 • Mawallafi Ibrahim Sani.
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Bvlm