Mnangagwa ya yi rantsuwar kama aiki | Labarai | DW | 24.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mnangagwa ya yi rantsuwar kama aiki

Sabon shugaban kasar Zimbabuwe Emmerson Mnangagwa, ya ce za a gudanar zaben kasar kamar yadda aka tsara yi a badi.

A jawabinsa na farko a matsayin shugaban Zimbabuwen jim kadan bayan shan rantsuwa, Mnangagwa ya bayyana aniyar farfado da harkokin arzikin kasar da ya shiga mawuyacin hali.

Shugaban Emmmerson Mnangagwa ya shaida wa 'yan kasar cewa, ''ina mai tabbatar maku a yau, za a gudanar da zaben kasa kamar yadda aka tsara, kuma shirye muke da mu martaba duk wani tsari na demokuradiyya''

Sabon shugaban an Zimbabuwe ya kuma yi alkawarin sake farfado da hulda da kasashen ketare, sai dai batutuwa da suka danganci mallakar filaye na gwamnatin baya dai ba za a sauya su ba.