1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ministocin kasashen Larabawa na taron gaggawa a Alkahira

July 15, 2006
https://p.dw.com/p/BuqR
Hoto: maec

A kuma halin da ake ciki ministocin harkokin waje na kungiyar kasashen Larabawa sun hallara a birnin Alkahira na kasar Masar don gudanar da wani taron gaggawa inda zasu tattauna kan hanyoyin da za´a bi don kawo karshen hare haren da Isra´ila ke kaiwa a Libanon da kuma a yankunan Falasdinawa. Jami´an diplomasiya sun ce ministocin na Larabawa zasu yi kira da a kawo karshen hare haren na Isra´ila kana kuma a samo hanyoyin lumanan warware rikicin Isra´ila da Hamas a hannu daya da kuma Isra´ila da Hezbollah a daya hannu. Da farko babban sakataren kungiyar ta kasashen Larabawa Amr Moussa ya ce ba daidai ba ne a rika zargin Syria da hannu a hare haren da sojojin Hezbolah ke kaiwa Isra´ila domin babu wata shaidar haka. Kasashen yamma dai na zargin mahukuntan birnin Damascus da marawa dakarun Islama na Hezbollah baya.