SiyasaTurai
Ministan Tsaron Birtaniya ya yi murabus
June 11, 2026
Talla
A cikin wasikar murabus dinsa, Healey ya zargi firaministan da ma'aikatar kudi da kasa samar da isassun kudaden da ake bukata domin kare kasar a daidai wannan lokaci da ake fuskantar karuwar barazanar tsaro.
Tun Watanni da dama da suka wuce, ma'aikatun tsaro da kudi na Birtaniya ke tattaunawa kan yadda za a samar da karin kudaden da ake bukata domin bunkasa karfin soji, lamarin da ya janyo jinkirin fitar da sabon shirin zuba jari a bangaren tsaro.
Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da sauye-sauyen siyasa da tsaro a duniya, tare da rage mayar da hankalin Amurka wajen kare kasashen Turai.