Miliyoyin yara ba sa zuwa makaranta a Gabas ta Tsakiya | Labarai | DW | 15.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Miliyoyin yara ba sa zuwa makaranta a Gabas ta Tsakiya

Asusun UNICEF ya ce rigingimu a yankin Gabas ta Tsakiya na kaiwo tsaiko a kokarin inganta fannin ilimin yara.

Asusun taimakon yara na Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF ya ce talauci da wariyar jinsi da kuma rigingimu da ake fama da su a yankin Gabas ta Tsakiya, sun hana yara fiye da miliyan 12 zuwa makaranta, duk da kokarin da ake na fadada fannin ba da ilimi. A cikin wani sabon rahoto da asusun na UNICEF ya bayar, ya ce akwai karin yara miliyan uku a kasashen Siriya da Iraqi da aka tilasta musu barin makaranta saboda rikicin da ake fama da su a yankin. Ko da yake rahoton na hadin guiwa da UNICEF da sashen kididdiga na hukumar ilimi, kimiyya da al'adu wato UNESCO suka wallafa ya ce yawan yaran da ke barin makaranta a yankin ya ragu, amma ana fuskantar tsaiko a shekarun baya bayan nan.