Merkel ta sanar da ministocinta na CDU | Labarai | DW | 25.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel ta sanar da ministocinta na CDU

A yunkurinta na kafa sabuwar gwamnati, shugaba Angela Merkel ta nada sabbin jini da 'yan mazan jiya a mukaman ministoci daga jam'iyyarta ta CDU

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta nada wani matashin dan siyasa a jam'iyyarta wanda kuma ke yawan sukar shugabar inda ta nada shi mukamin minista a sabuwar gwamnati.

Matashin dan siyasar Jens Spahn mai shekaru 37 da haihuwa zai rike mukamin ministan lafiya.

Matakin dai ya nuna aniyar shugabar na shigar da masu sukar lamirinta a cikin gwamnati domin tafiya tare.

sauran nade naden sun hada da Julia Kloeckner wadda aka nada ministar ayyukan noma da kuma Anja Karliczek ministar Ilmi.