MDD za ta kwashe jami′anta a Yemen | Labarai | DW | 03.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

MDD za ta kwashe jami'anta a Yemen

Majalisar Dinkin Duniya za ta kwashe ma'aikatanta na agaji akalla 140 wadanda ke aiki a Sana'a babban birnin kasar Yemen saboda kazantar da rikici ya yi a birnin.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana shirinta na kwashe ma'aikatanta na agaji akalla 140, wadanda ke aiki a Sana'a babban birnin kasar Yemen saboda kazantar da rikici ya yi a birnin. Bayanan da ke fitowa daga Yemen dai na nunin cewa sabon rikicin ya kaiga datse hanyar zuwa babban filin jirgin saman birnin na Sana'a.

Cikin daren da ya gabata ne wasu jirage suka yi ruwan bama-bamai a yankunan da mayakan Houthi ke da rinjaye, matakin da ke zama na dafa wa magoya bayan tsohon shugaba Ali Abdallah Saleh. Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce rayuka da dama ne suka salwanta cikin kwanaki hudun da aka kwashe ana musayar wuta tsakanin bangarorin da ke gaba da juna.

Wasu rahotannin da ke fitowa daga Djibouti sun tabbatar da ganin wasu jiragen da aka tanadar saboda daukar ma'aikatan Majalisar ta Dinkin Duniya daga Yemen din.