MDD ta bukaci bai wa fararen hula kafa a El-Fasher na Sudan
October 27, 2025
Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiran da a bude hanyoyi ga fararen hula da suka makale ko suke tserewa daga birnin El-Fasher na kasar Sudan, bayan dakarun RSF suka bayyana sun karbe iko da birnin a jiya Lahadi.
Shugaban sashen agajin jin kai na Majalisar Dinkin Duniya, Tom Fletcher, ya bayyana damuwarsa kan rahotannin kashe-kashen fararen hula a El-Fasher, birnin da shi kadai ne ya rage a yammacin Darfur ba tare da fadawa hannun mayakan RSF ba kafin yanzu.
Mista Fletcher ya ce dubban fararen hula sun makale cikin yunwa da fargaba, ba kuma tare da samun abinci ko kula da lafiya da tsaro ba.
Rahotanni dai sun nuna cewa sama da mutane dubu 260, rabinsu kananan yara ne suka makale a cikin birnin na El-Fasher ba tare da wata hanyar samun abinci ko taimako ba.