MDD: Ta ce Buhari ya yi ba daidai ba | Labarai | DW | 11.02.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

MDD: Ta ce Buhari ya yi ba daidai ba

Majalisar Dinkin Duniya ta ce Muhammadu Buhari ya taka doka ta kasa da kasa a game da 'yancin shari'a da kuma raba shari'a da mulkin zartaswa bayan da ya dakatar da aikin alkalin alkalai na kasar Walter Onnoghen.

Wani mai magana da yawun Majalisar Dinkin Duniyar Diego Garcia Sayan ya ce dokar kasa da kasa da ta yi daidai da ta kare hakin bil Adama ta ce ba za a iya cire alkali ba a kan aikinsa idan ba wata babbar tabargaza ya yi ba, ko ya nuna gazawa a game da aikinsa. Sannan ya ce duk wani hukumci mai kama da irin wannan, sai majalisar alkalai ko wata hukuma ta musammun kan iya daukar mataki a kai.