1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTimor ta Gabas

MDD ta bukaci Isra'ila ta fice daga Tuddan Golan

December 3, 2025

Isra'ila ta mamaye Tuddan Golan ne tun a shekarar 1967 kuma ta hada shi cikin kasarta a 1981.

https://p.dw.com/p/54fJ6
Isra'ila ta mamaye Tuddan Golan ne a shekara 1967
Isra'ila ta mamaye Tuddan Golan ne a shekara 1967Hoto: Bakr Alkasem/AFP

Majalisar Dinkin Duniya ta amince da wani kuduri da ke neman Isra'ila ta janye daga Tuddan Golan, wani yanke da kasar ta kwace tare da mamaye a gomman shekaru da suka gabata.

An amince da kudurin ne da kuri’u 123 a yayin da bakwai kacal ke adawa da matakin, ciki har da Isra'ila da Amurka, sannan kasashe 41 kuma suka kaurace wa kada kuri'a.

Siriya ta gargadi Isra'ila ta janye dakarunta a Tuddan Gola

Tuddan Golan ko kuma Golan Heights, wani muhimmin tsauni ne mai tudun  kilomita 60 da kuma kilomita 25 na faɗi.

A cikin kudurin, Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana matakin Isra’ila na 1981 na kakaba wa yankin dokokinta, da tsarin mulkinta a matsayin haramtacce tare da yin kira da a soke matakin.

Juya baya ga Donald Trump kan Tuddan Golan

Jakadan Isra’ila a MDD, Danny Danon, ya wallafa a shafinsa na X cewa “Majalisar Dinkin Duniya ta sake nuna yadda ta ke nesa da hakikanin gaskiya."