1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD: Myanmar na muzguna wa 'yan Rohingya

March 7, 2018

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kasar Myanmar ta kaddamar da wani kamfe na ta'addanci kan musulmi 'yan Rohingya, tare ma da azaftar da su da tsananin yunwa, a ci gaba da manufar shafe su daga doron kasa.

https://p.dw.com/p/2toed
Bangladesch Rohingya-Flüchtlinge in Palong Khali
Wasu daga cikin musulmi 'yan Rohingya da ke cikin mawuyacin haliHoto: picture-alliance/dpa/B. Armangue

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kasar Myanmar ta kaddamar da wani kamfe na ta'addanci kan musulmi 'yan Rohingya, tare ma da azaftar da su da tsananin yunwa, a ci gaba da manufar shafe su daga doron kasa da kasa ke yi. Mataimakin sakataren Majalisar Dinkin Duniyar kan harkikin kare hakkin jama'a, Andrew Gilmour shi ne ya sake nanata aniyar kasar ta Myanmar kan musulmin marasa rinjaye.

Kimanin musulmin na Bama dubu 700 ne suka tsere zuwa kasar Bagaladash cikin watan Agustan bara, bayan tashin wata hatsaniya tsakaninsu da sojojin kasar. Su dai musulmin na Rohingya sun fusknaci tsana daga gwamnatin kasar ne inda suke zama ba tare da mallakar takardun zama 'yan kasar ba. Ana kuma yi masu kallon bakin haure ne daga Bangaladash a kasar ta Myanmar, duk da cewar galibinsu na kasar ne tsawon shekaru.