MDD: An samu tashin farashin abinci a Afika
April 17, 2021Tashin farashin wanda ba a ga irin sa ba kusan shekaru goma a cewar hukumar kula da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, ya kai sama da kashi 30%, inda baya ga matsalar coronar akwai ma ta ragowar da aka samu wajen samun amfanin gona a daminar bana.
A wani hasashen da ta yi, Majalisar Dinkin Duniyar ta yi bayanin cewa mutum miliyan 31 za su fuskanci karancin abinci a yammacin na Afirka a tsakanin watan Yuni zuwa Agustan wannan shekara.
Hakan kuma kamar yadda ta nunar, zai iya haddasa wasu matsalolin lafiya masu bukatar daukin gaggawa, kari a kan annobar corona da ma saurarn nau'uka na rikice-rikice da ake fama da su a wasu kasashen yammacin na Afirka.
A halin yanzu dai farashin abinci kamar shinkafa da sauran tsaba, ya tashi ne da sama da kashi 40%, tashin da ba a gani ba a wasu kasashen yankin shekaru sama da biyar.